Gwamna ya bukaci Buhari ya kafa cibiyar gyaran tunanin masu cin hanci

Gwamna ya bukaci Buhari ya kafa cibiyar gyaran tunanin masu cin hanci

- Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bukaci shugaba Buhari ya gina wata cibiyar saita tunanin masu cin hanci

- Ya ce aikin cibiyar shine gyara da saita tunanin 'yan siyasar dake assasa cin hanci da rashawa

- Bello ya yi wannan kira ne yayin jawabi ga wasu magoya bayan jam'iyyar APC a Lokoja

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bukaci shugaba Buhari ya gina wata cibiya da za ta ke gyara da saita tunanin 'yan siyasar dake assasa mummunar dabi'ar nan ta cin hanci da rashawa a Najeriya.

Gwamna ya bukaci Buhari ya kafa cibiyar gyaran tunanin masu cin hanci

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

Bello ya yi wannan kira ne yayin gabatar da jawabi ga wasu magoya bayan jam'iyyar APC a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Duba hotunan El-Rufa'i a kasar Saudiyya domin addu'o'i ga Najeriya

Da yake fadar illolin cin hanci, gwamna Bello, ya ce masu cin hanci da rashawa sun fi mayakan kungiyar Boko Haram illa.

Kazalika gwamnan ya zargi jam'iyyar PDP da dasa tsiron cin hanci da yanzu ya girma ya fitar da rassa ko ina cikin fadin Najeriya.

A cewar Bello, jagorancin shugaba Buhari ne kadai zai iya fitar da Najeriya daga kangin fatara da talauci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali
NAIJ.com
Mailfire view pixel