Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani

Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani

- Gwamnatin Kasar China ta kafa dokar hana 'ya'yan Musulmi zuwa Islamiyya da kuma karatun Kur'ani

- Dokar da ya fito da aka kafa a yankin Linxia zai fara aiki ne a farkon watan Febrairu mai zuwa

- Wannan dai ba shine karo na farko da Kasar ta Sin ke musgunawa musulmi da musulunci ba

A yayin da addinin musulunci ke kara samun karbuwa wasu kasashen turai kamar Ingila da sauran su, gwamnatin Kasar Sin ta haramtawa al'ummar musulmi da ke zaune a da'irar Gansu zuwa makarantun Islamiyya har ma da karatun Al-Kur'ani mai girma.

Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani

Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani

Sanarwan ya fito ne daga Ofishin ilimi na garin Linxia, inda ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Fabrairun 2018.

KU KARANTA: Kungiyar CAN ta zargi shugabanin addinin musulunci da goyon bayan makiyaya

Adadin al'ummar Musulmi mazauna wannan yankin ya kai a kalla miliyan daya dukannin su yan kabilar Hui ne marasa rinjaye.

Wannan dai ba shine ne farau ba, dama Kasar ta Sin tayi kaurin suna wajen muzguwa na mabiya addinin Musulunci, musamman mazauna yankin Xinjiang wanda musulmi ne suka fi rinjaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali
NAIJ.com
Mailfire view pixel