Makiyaya sun kai wani sabon hari kan malaman makaranta a jihar Ogun

Makiyaya sun kai wani sabon hari kan malaman makaranta a jihar Ogun

A halin yanzu wasu malamai biyu na makarantar firamare a jihar Ogun, su na fafautikar tseratar da rayukan su a gadon wani asibitin gwamnati, a sakamakon harin makiyaya da ya gadar musu da munanan raunuka a ranar Alhamis din da ta gabata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan hari ya afku ne a kilomita kadan da makarantar wannan malamai dake karamar hukumar Eworoko ta Arewa, inda mazauna suka shiga cikin razani da har makarantu makusanta suka sallami daliban su cikin gaggawa domin gujewa abin da ka iya biyo baya.

NAIJ.com ta fahimci cewa, wannan hari ya afku ne bayan 'yan lokuta kadan da shigar malaman makaranta domin fara gudanar da darussa ga dalibai.

Makiyaya

Makiyaya

Shugaban karamar hukumar, Mista Kehinde Adepegba, shine ya tabbatar da wannan rahoto ga manema labarai na jaridar Punch, inda ya bayyana cewa tuni an garzaya da malaman biyu asibitin domin jibintar lafiyarsa.

KARANTA KUMA: Buhari ya shirya wa shan kashi a zaɓen 2019 - Ekweremadu

Sai kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya kara tabbatar da ingancin rahoton, inda yace hukumar ta fara gudanar da bincike domin bankado masu hannu wajen aikata wannan ta'addancin.

Abimbola ya kara da cewa, ko shakka babu wannan hari na 'yan cikin gida ne ba bakin haure ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel