Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ƙara wa 'yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan

Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ƙara wa 'yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan wata sabuwar doka ta ƙara wa 'yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan.

Wannan doka ta baiwa 'yan majalisun tarayya da kuma na jihohi wata dama ta kare su daga duk wani laifukan furuci da suka aikata, inda ta kuma faɗaɗa ikonsu na umartar jami'ai wajen cafke duk wani da ya saɓawa dokokin su.

Shugaban kasa; Muhammadu Buhari

Shugaban kasa; Muhammadu Buhari

NAIJ.com ta kuma fahimci cewa, dokar ta bayar da iko ga 'yan majalisu na kiranyen duk wani mutum ya gurfana a gaban su domin bayar da wata shaida akan kowane bincike da suke gudanarwa.

KARANTA KUMA: Almundahanar N11bn: Kotun ƙoli ta umarci Shema ya fuskanci shari'a

Jaridar Daily Trust ta ruwaito da sanadin hadimin shugaban ƙasa akan harkokin majalisun tarayya, Sanata Ita Enang, inda ya bayyana cewa shugaban ya kuma rattaba hannu a kan wasu sabbin dokoki bakwai da 'yan majalisun su ka buƙata.

A ranar da ta gabata ne kuma, NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya rattaba hannu ne akan wanni sabbin dokoki 8 kafin ya garzaya birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha domin halartar taron shugabannin ƙasashen nahiyyar Afirka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel