Yanayin wutar lantarki zai nagartu cikin 'yan shekaru kaɗan

Yanayin wutar lantarki zai nagartu cikin 'yan shekaru kaɗan

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa, jajircewa tare da hoɓɓasan gwamnatin tarayya zai tabbatar da ingantacciyar wutar lantarki a ƙasar nan cikin 'yan shekaru kaɗan masu gabatowa.

Ya kuma bayyana cewa, faɗi tashin da gwamnatin tarayya take zai tabbatar da tsaro mai tsanani cikin ƙanƙanin lokaci a faɗin ƙasar nan.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a wata liyafar dare da aka shirya a yayin halartar taron tattalin arziki na duniya, wanda aka gudanar a birnin Davos na ƙasar Switzerland a ranar larabar da ta gabata.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Osinbajo da sanadin hadimin sa na musamman akan hulɗa da manema labarai, Mista Laolu Akande ya bayyanawa manema labarai cewa, cikin wasu 'yan shekaru kaɗan yanayin wutar lantarki na Najeriya zai fuskanci juyin juya hali na nagarta tare da inganci.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun kai wani sabon hari jihar Binuwai

Akande ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya ta duƙufa wajen magance muhimman matsalolin da take fuskanta a halin yanzu da suka haɗar da matsalar wutar lantarki da kuma harkar tsaro a ƙasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel