Gusau: Gwamnatin Zamfara ta sanar da daukar ma'aikatan likitoci

Gusau: Gwamnatin Zamfara ta sanar da daukar ma'aikatan likitoci

Gwamnatin jihar Zamfara tace za ta dauki karin ma'aikatan likitoci da na jinya da kuma ungozoma a cikin sashen kiwon lafiya na jihar don magance matsalar rashin isashen ma’aikatan lafiya a wuraren kiwon lafiyar a fadin jihar.

Kwamishinan kiwon Lafiya na jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman, ya sanar da daukar ma'aikatan likitoci da na jinya da kuma ungozoma a cikin sashen kiwon lafiya na jihar, ya ce za a fara daukan ma’aikatan a ranar Litinin.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Liman ya bayyana wannan labari ne a Gusau a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu a wata ganawa da haɗin gwiwar abokin ciniki ta sashen kiwon lafiya wanda ma'aikatar Lafiya ta shirya.

Ya ce gwamna Abdul'aziz Yari kwanan nan ya amince da daukar nauyin likitoci da ma'aikatan jinya a hukumar kula da ayyukan asibitin jihar.

Gusau: Gwamnatin Zamfara ta sanar da daukar ma'aikatan likitoci

Gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari

A cewarsa, gwamnati za ta yi amfani da ita wajen magance matsalar rashin isashen ma’aikatan lafiyar a wuraren kiwon lafiyar jihar.

KU KARANTA: Abin da ya sa na gana da Maina a Kasar waje – Ministan shari'a Malami

Kwamishinan ya bayyana cewa, ganawar da abokan hulɗar kiwon lafiyar sun yi ne don su fahimci kokarin da suke yi wajen tallafawa gwamnatin jihar wajen inganta aikin kiwon lafiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere
NAIJ.com
Mailfire view pixel