Hukumar EFCC ta daskarar da asusun ajiyar tsohon Sakataren gwamnati, Babachir Lawal

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun ajiyar tsohon Sakataren gwamnati, Babachir Lawal

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa tare da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC ta daskare asusun ajiyar kudi na banki mallakin tsohon Sakataren gwamnatin tarayyar, Mista Babachir Lawal.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu mataki ne da hukumar ta dauka musamman ma domin samun sukunin cigaba da binciken da suke yi masa na handame kudin kasa.

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun ajiyar tsohon Sakataren gwamnati, Babachir Lawal

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun ajiyar tsohon Sakataren gwamnati, Babachir Lawal

KU KARANTA: Jam'iyyu 30 sun shirya kada Buhari a 2019

NAIJ.com ta samu daga wata majiyar sirri cewa asusun bankunan da aka rufe na tsohon sakataren gwamnatin sun hada da na bankin Sky da kuma Diamond.

A wani labarin kuma, Akalla mutane uku suka sha harsashen bindigar jami'an 'yan sandan nan na Najeriya ya runduna ta musamman dake yaki da fashi da makami watau Special Anti-Robbery Squad, SARS shiyyar jihar Plateau, garin Jos a wata mashayar jiya.

Lamarin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin sun tabbatar da cewa ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata kuma wadanda aka harba din sun hada da Dung Chung, dan shekaru 42 dake sana'ar kafinta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali
NAIJ.com
Mailfire view pixel