Buhari ya gana da wasu gwamnoni a Aso Villa

Buhari ya gana da wasu gwamnoni a Aso Villa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da wasu mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), a fadar shugaban kasa, shugaban kungiyar, Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya jagoranci tawagar gwamnonin.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu ya gana da wasu gwamnoni a Aso Villa, Abuja.

A cewar rahotanni, taron da ya fara a daidi karfe 2:00 na rana, ya samu halartar gwamnonin shida.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Udom Emmanuel na Akwa Ibom da Dave Umahi na Ebonyi da Aminu Masari na Katsina da Simon Lalong na Filatu da Atiku Bagudu na Kebbi da kuma Abdulaziz Yari na Zamfara.

Yanzu-Yanzu: Buhari yana ganawa da wasu gwamnoni a Aso Villa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tare da wasu gwamnoni a Aso Villa

Idan dai baku manta ba NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban Buhari a ranar Alhamis kafin ganawarsa da gwamnonin ya jagoranci zaman taron tsaro inda aka tattauna game da yanayin tsaro a fadin kasar.

KU KARANTA: Abunda shugabannin jami'an tsaron Najeriya suka tattauna da Buhari

Taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa ta samu halartar shugabanni NSA, NIA da ministan tsaro.

.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel