Za mu ƙauracewa cin naman shanu - Al'ummar kudancin Najeriya

Za mu ƙauracewa cin naman shanu - Al'ummar kudancin Najeriya

Wasu ƙungiyoyi biyu na Najeriya da suka hadar da ƙungiyar kudanci da kuma Najeriya ta tsakiya, sun yi kira ga al'ummominsu na ƙasar nan akan su ƙauracewa cin naman shanu har na tsawon kwanaki 21 domin jimamin wadanda hare-haren makiyaya ya afkawa.

Ƙungiyoyin sun yi wannan kira ne a ranar larabar da ta gabata a wani taro da suka gudanar a birnin Enugu, inda zasu fara gudanar da wannan yaji na cin nama daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2018.

Shanu a wurin kiwo
Shanu a wurin kiwo

Rabaran Okechukwu Obioha da kuma Rabaran James Pam sune suka wakilci ƙungiyoyi biyun wajen yanke wanna hukunci domin jimamin wadanda ibtila'in hare-haren makiyaya ya afkawa.

KARANTA KUMA: Obasanjo ba shi da lokacin lura da ƙoƙarin Buhari akan tattalin arziki

Ƙungiyoyi biyun sun kuma nuna rashin amincewar su da mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osinbajo, a matsayinsa na jagoran kwamitin kawo ƙarshen rikicin makiyaya a ƙasar nan, inda suka buƙaci gwamnati tayo aringizon dakarun soji domin fuskantar ƙalubalen.

Sun kuma nemi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akan ya tabbatar da damƙa tare da gurfanar da duk masu riƙe da makamai wajen aikata akan al'ummar jihar Binuwai da sauran sassan ƙasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel