An rasa wanda zai bada shaida a shari'ar tsohon gwamnan Abia

An rasa wanda zai bada shaida a shari'ar tsohon gwamnan Abia

Wani lauya, Kingsley Ekwem, ya ki yarda da bayar da shaida a gaban kotun da ake gudanar da shari'ar tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Orji Uzor Kalu da wasu mutane biyu da ake zargin su da laifin zambar naira biliyan 3.2

A madadin haka, lauyan ya nemi alkalin kotun ta tarayya dake jihar Legas, Mohammed Idris, akan yayi watsi da takardar gabatar da shaida kamar yadda hukumar EFCC ta bukaci kotun ta tursasa shi don tabbatar da gaskiyar lamarin.

Lauyan ya bayyana cewa, ba zai yiwu ya kasance mai bayar da shaida ba a sakamakon dangartakar dake tsakanin sa da wadanda yake karewa ba da kuma cibiyar shari'a da yake wakilta ba.

Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu

Ya kara bayyanawa kotun cewa, a sakamakon dama da kundin tsare-tsare na shari'a ya gindaya, kotun ba ta hurumin tursasa sai ya kasance mai bayar da shaida a gabanta.

KARANTA KUMA: Hular kamfe din shugaba Buhari ta bayyana a zaman majalisa

Sai da shi kuma lauya mai wakiltar hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya yi jayayya da wannan batu na lauyan tsohon gwamna Kalu, inda yace wannan doka ba ta haramtawa lauyoyi kasancewa shaidu a gaban kotu ba.

Tsohon lauya mai wakilta Kalu, Awa Kalu ya gargadi kotun cewa, ka da ta tursasa lauyan akan bayar da shaida domin haka zai zamto tufka da kuma warwara a sakamakon kare tsohon gwamnan da yake yi, inda alkali mai shari'a ya daga sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali

Kishin-kishin: Jam'iyyar APC na shirin yi wa wasu jiga-jigan ta kora da hali
NAIJ.com
Mailfire view pixel