2019: Abubuwan da Obasanjo ya gaya wa shugaba Buhari a wasikarsa don kar yayi takara

2019: Abubuwan da Obasanjo ya gaya wa shugaba Buhari a wasikarsa don kar yayi takara

- An ga alamar shugaba Buhari na son takara a zagaye na biyu

- Bashi da cikakkiyar lafiya, inji Obasanjo

- Ka koma gida ka huta, kayi iya yinka, Najeriya ta fi karfinka

2019: Abubuwan da Obasanjo ya gaya wa shugaba Buhari a wasikarsa don kar yayi takara
2019: Abubuwan da Obasanjo ya gaya wa shugaba Buhari a wasikarsa don kar yayi takara

Kamata yayi ace Najeriya Ana yin 25/7, ba 24/7 ba, inji Obasanjo. Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi bayani a cikin wata wasika, game da matsalolin dake damun Najeriya, sannan ya kawo hanyoyin da za abi domin magance matsalolin.

A cikin wata wasika mai suna, “The Way Out: A Clarion Call for Coalition for Nigeria Movement” a ranar talatar nan 23 ga watan Janairun nan tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi magana game da harkokin siyasar kasar nan, sannan ya nuna yanda ya goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo yace ko kadan baya dana sanin goyan bayan daya bawa shugaba Buharin.

Inda yace shugaba Buharin yana yiwa kasar nan aiki sosai, ya kara da cewa jam’iyar APC ba ita ce mafita ga ‘yan Najeriya ba. Ya bada shawara ga hadin kan ‘yan Najeriya, inda yace duk wani mai kishin kasa zai yi kokarin bada goyon baya. Ya ce hadin kan ba wai irin hadin kai na siyasa ba, hadin kai ne wanda za’ayi da zai ci da kasar mu gaba. 

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: SLS na so a dau mataki kan ta kwabe

“Kamata yayi muyi wa junan mu fatan alkhairi, a wannan sabuwar shekara da muke ciki. Bada son raina na rubuta wannan wasikar ba, sai dan irin yanayin da kasar mu take ciki. Wasu na iya tambaya, 'menene ya faru Obasanjo ya rubuta irin wannan muhimmiyar wasika', kuna da damar yin irin wannan tambayar. 

Halin da kasar nan take ciki na talauci, rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da rashin cigaba na siyasa sune su kai mana katutu a kasar nan. 

Shekaru hudu da suka wuce, a lokacin dana yaga katina na PDP, na fito fili nayi bayani cewar na bar siyasa, amma halin da kasar mu Najeriya take ciki, yasa na tsaya a matsayin da nake, kuduri na biyu da majalisar dinkin duniya ta dauka shine na kawar da yunwa nan 2025, shekaru biyar da suka wuce, ina daya daga cikin wanda suka jagoranci zuwa wasu jahohi saboda kadamar da harkar ilimi, da aikin yi ga matasa.

Ina daya daga cikin wanda suka dinga bawa mutane shawara da kuma kokarin karfafawa mutane gwiwa, musamman wanda suka fidda rai da kauna. 

Nayi imanin cewar Najeriya mu na da arzikin da bai kamata ace wasu suna cikin halin kaka na kayi ba. Obasanjon ya rufe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel