Allah ya kyauta! Kannen miji sun hallaka matar yayansu a Katsina

Allah ya kyauta! Kannen miji sun hallaka matar yayansu a Katsina

Rikici tsakanin uwar miji da matar danta ya yi sanadiyar da kannen miji suka hallaka matar yayansu.

Mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, a karamar hukumar Dan Ja dakejihar Katsina.

Marigayiyar da aka ambata da suna Hadiza Salisu Dan kasuwa, ta samu sabani da uwar mijinta da suke zama tare a gida daya a garin Layin Mahuta dake cikin karamar hukumar Dan Ja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya tabbatar da afkuwar a’lamarin, inda ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa cacar-baki aka yi tsakanin matar da uwar mijinta.

Ya ce, uwar mijin ce ta yi zargin cewa surukarta ta ta zage ta, dalilin da ya sa kannen mijin biyu, Shafi'u Ibrahim da Fahad, suka fusata a kan an zagi mahaifiyarsu.

Allah ya kyauta! Kannen miji sun hallaka matar yayansu a Katsina
Allah ya kyauta! Kannen miji sun hallaka matar yayansu a Katsina

A cikin dare suka je suka sami matar dan uwan nasu suka ma ta duka da itace har sai da ta kai tana zubar da jini har ta rasu" kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

An dauki gawarta an kai babban asibiti na funtua, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta. An kuma yi jana'izar matar a ranar Litinin 22 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama wani mutum mai shekaru 30 kan zargin lalata yar shekara 13 a Nasarawa

A halin da ake ciki 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike bayan sun kama kannen mijin biyu wadan da yanzu ake tsare da su a hedikwatar 'yan sanda da ke Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel