Bakadalar $44m: EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar NIA, Ambasada Dauda

Bakadalar $44m: EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar NIA, Ambasada Dauda

- EFCC ta gayyaci tsohon mukaddashin hukumar NIA akan wasu kudade da suka bace a asusun ajiya hukumar

- An sace kudaden ne watanni biyu bayan shugaba Buhari ya sauke Ayodele Oke daga mukmin shugaban hukumr NIA inji wani jami'in hukumar EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar lekan asiri (NIA), Ambasada Mohammad Dauda, a karshen makon da ya gabata.

Legit.ng ta rawaito labarin yadda dala miliyan $44m suka bace daga asusun ajiyan hukumar NIA dake Abuja watanni biyu bayan an sauke tsohon shugaban hukumar NIA, Ayodele Oke.

Bakadalar miliyan $44m : EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar NIA, Ambasada Dauda
Bakadalar miliyan $44m : EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar NIA, Ambasada Dauda

Wani babban jami’in tsaro ce, an cire makuda kudaden ne daga asusun NIA kafin aka nada Ahmed Rufai Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar.

KU KARANTA : Gusau: Gwamnatin tarayya za ta ceto masana'antu a Zamfara

An ga Ambasada Dauda, wanda ya rike mukamin mukkadashin hukumar NIA bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke, Oke, a ofishin hukumar EFCC a ranar Juma’a da ranar Asabar.

Wani jami’in hukumar EFCC yace zai yiwu gayyatar da aka yiwa ambasada Dauda yana da alaka da kudaden da suka bace a asusun ajiyan hukumar NIA.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel