Laifin abokan hamayyan Buhari ya kamata a gani kan rashin tsaro – Sarkin Katsina

Laifin abokan hamayyan Buhari ya kamata a gani kan rashin tsaro – Sarkin Katsina

Sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman, ya daura laifin kalubalen da tsaro ke fuskanta a kasar akan ayyukan abokan adawan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Usman, hankalin yan adawan shugaban kasa bai kwanta da yadda yake kokarin ganin ya sabonta al’amuran kasar ba.

A wani jawabi daga mataimakin gwamnan Katsina a kafofin watsa labarai, Abdu-Labaran Malumfashi, ya ce basaraken ya yi wannan hasashe ne a ranar Asabar lokacin da shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, tare da Gwamna Aminu Masari suka kai masa ziyarar ta’aziyya kan rasuwar tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Lawal Kaita.

Laifin abokan hamayyan Buhari ya kamata a gani kan rashin tsaro – Sarkin Katsina
Laifin abokan hamayyan Buhari ya kamata a gani kan rashin tsaro – Sarkin Katsina

Basaraken ya bukaci gwamnati da karda ta daga kafa sannan kuma ta hukunta duk wanda aka samu da aikata miyagun laifuka dake barazana ga zaman lafiyar kasar.

KU KARANTA KUMA: Kano 2019: Sabon rikici na shirin barkewa yayinda magoya bayan Ganduje da Kwankwaso zasu yi gangami a rana daya

Ya kara da cewa ya zama dole gwamnati ta yi hukunci akan duk wani mutun ko kungiya da ta samu da hannu akan ayyukan ta’addanci, rikicin makiyaya da manoma, da kuma sace-sacen mutane duk kuwa matsayin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel