Jama’atul Nasril Islam ta fallasa karyar Kungiyar CAN

Jama’atul Nasril Islam ta fallasa karyar Kungiyar CAN

- Kungiyar Musulmai tayi tir da Kungiyar Kiristocin Najeriya na CAN

- Kungiyar tace an saba damke Kiristoci da barna amma CAN tayi gum

- Har wa yau an kashe Musulmai da dama amma ‘Yan CAN sun yi tsit

Kungiyar Musulman kasar nan ta JNI ta maida martani ne ga wani jawabi da Sakataren Kungiyar CAN watau Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da yi wa Kiristocin Najeriya kisan mummuke.

Khalid Aliyu yace karya CAN din ta yi kuma dole a bayyana ba don kare Gwamnati ba sai dai don kare Musulmai daga sharrin da aka yi masu. JNI tace ba ta manta da lokacin da wani Fasto yayi kira a kashe Fulani ba a kasar nan.

Jama’atul Nasril Islam ta fallasa karyar Kungiyar CAN
Jama’atul Nasril Islam ta ja hankalin Sakataren CAN

Bayan nan kuma Malam Khalid yace akwai lokutan da aka rika kama Kiritoci su na kokarin kona coci da sunan Musulmai a Najeriya amma CAN tayi shiru. Ko a Jihar Benuwe dai an samu wadanda ba Musulmai ba su na ta’adi.

KU KARANTA: Yadda Gwamnan Ortom ke hura wutan rikicin Jihar Benuwe

A cewar Kungiyar ta Jam’atul Nasril Islam, CAN na kokarin juya lamarin ne don kuwa ko a kwanan nan an kai hare-hare a irin su Jihar Ribas amma CAN ta maida hankali kan kashe-kashen da aka yi a Jihar Kwara da sauran su.

An kashe Musulmai da dama a irin su Taraba da Kaduna da ma Jihar Katsina amma Kiristocin kasar sun yi tsit ba su ce uffan ba. Kungiyar ta JNI ta gargadi Fastocin kasar nan da ke kalamai na tada fitina su kula da bakin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel