Ana shirin tsaida Dangiwa Umar takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa

Ana shirin tsaida Dangiwa Umar takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Ana zuga Kanal Dangiwa Umar ya fito takarar Shugaban kasa

- Tsohon Gwamnan na iya kawowa Shugaba Buhari cikas a 2019

- Masu harin kujerar Shugaban kasa daga Arewa sun kara yawa

Yayin da siyasar 2019 ta ke kara karasowa mun samu labari cewa an kawo wanda ake sa ran zai takawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari burki daga Yankin Arewacin Najeriya a zabe mai zuwa.

Ana shirin tsaida Dangiwa Umar takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa
Dangiwa Umar zai yi takarar Shugaban kasa a 2019

Wani tsohon Sojan kasar nan watau Kanal Dangiwa Umar ne wasu ke tunanin zai iya karawa da Shugaban kasa Buhari. Dangiwa Umar (rtd) mutum ne mai mutunci da kima a idon Jama'a. Umar kuma ya yarda da hadin kan Najeriya.

KU KARANTA: Wani Sanata ya kare Shugaban kasa Buhari a Majalisa

Legit.ng ta samu labari cewa wasu masana a Kasar su na ganin Dangiwa Umar zai fito ne a karkashin tutar wata Jam'iyya mai suna NIM. Kanal Dangiwa yayi Gwamna a lokacin mulkin Sojin Janar Babangida kuma ba a san shi da wasa ba.

Idan dai haka ta tabbata, masu neman kujerar Shugaban kasa daga Yankin Arewa sun karu. Yanzu haka akwai irin su Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Sule Lamido, Ibrahim Shekarau da sauran su da ba mamaki su na harin 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel