Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Fitaccen jarumin nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Rabi'u Rikadawa ko kuma 'Dila' kamar yadda ake kiran sa a tsakanin abokan sana'ar sa ya bayyana cewa ya ji dadi da gwamnan Kano ya yafewa jaruma Rahma Sadau.

Rabi'u Rikadawa ya bayyana cewa hakika yafiyar da aka yi wa jarumar abu ne mai kyau kuma wannan ya nuna cewa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje cikakken shugaba ne mai sauraren talakawan sa.

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa jarumin ya kuma bayyana cewa daman dai duk dan adam ajizi ne kuma ya kamata idan mutun yayi laifi sannan kuma ya roki yafiya to a yafe masa domin samun maslaha.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar masu shirya fina-finai watau MOPPAN tayi fatali da batun yafiyar da akayi wa jarumar inda ta kuma ce ita sai kotu zata raba su.

Tun farko dai a shekarar da ta gabata ne aka dakatar da jarumar daga dukkanin fina-finan Hausa saboda ta rungumi wani mawaki yayin da suke daukar wata wakar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel