Gwamnatin Jihar Borno ta dage dokar takaita yawo a Maiduguri da Jere

Gwamnatin Jihar Borno ta dage dokar takaita yawo a Maiduguri da Jere

- An dage dokar daga karfe 8 na yamma zuwa 10:30 na yamma

- Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar, Mohammed Bulma, shi ne ya sanar da hakan

- Kwamishinan ya yabawa mutane game da hadin kan da su ke ba wa jami'an tsaro

Gwamnatin Jihar Borno ta dage dokar takaita yawo na tsawon makwanni 3 da ta gindiyawa Maiduguri da Karamar Hukumar Jere ta Jihar. Dokar a makwanni 3 da su ka gabata, ya na farawa ne daga karfe 8 na yamma ya kare da karfe 6 na safe.

Kwamandan Aikin Soja na Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Rochas, shi ne ya kakaba dokar a ranar 5 ga watan Janairu. Daga ranar 20 ga watan Janairu. A yanzun b kuwa dokar ta na farawa ne daga karfe 10:30 na yamma ta kare da karfe 6 na safe.

Jihar Borno ta dage dokar takaita yawo a Maiduguri da Jere
Jihar Borno ta dage dokar takaita yawo a Maiduguri da Jere

KU KARANTA: Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

Jaridar Ledership Weekend ta tunatar da mu cewar Kwamandan shi ne ya nemi zafafa dokar fiye da yadda ta ke a baya don su samu isasshen lokacin yaki da 'yan Boko Haram da sauran 'yan ta'adda.

Sai ga shi a jiya, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Labarai da Al'adu na Jihar, Mohammed Bulama ya sanarwa manema Labarai sabon tsarin. A madadin Gwamnatin Jihar, Bulama ya ba wa jama'a hakuri game da wannan doka.

Ya kuma yabama jama'a ga irin hadin kan da su ke bayarwa ga jami'an tsaro. Ya kuma kara jawo hankulan su da su cigaba da bayar da hadin kan. Ya kuma yi masu albishir da cewan da yardar Allah nan ba dadewa ba za a magance matsalolin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel