Mafi kyawun buri a rayuwata shine yiwa Najeriya da shugaba Buhari hidima - Ahmed Rufa'i Abubakar

Mafi kyawun buri a rayuwata shine yiwa Najeriya da shugaba Buhari hidima - Ahmed Rufa'i Abubakar

Mista Ahmad Rufa'i Abubakar, sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasa wato National Intelligence Agency (NIA), ya bayyana cewa mafi kyawun burin sa a rayuwa shine yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari hidima da kuma Najeriya.

A wata sanarwar ranar asabar ta yau da sanadin mataimakin shugaban labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, ya bayyana cewa sabon shugban na NIA ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, a yayin wata liyafa ta rabuwa da hadimai tare da ma'aikatan fadar shugaban suka shirya masa a fadar dake Abuja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kafin wannan sabon nadin mukami da Mista Abubakar ya samu, ya kasance babban hadimi na musamman ga shugaban kasa a kan harkoki da al'amuran kasashen waje a ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Ahmed Rufa'i Abubakar
Ahmed Rufa'i Abubakar

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shine ya bude taron liyafar da jawabai, inda ya bayyana Mista Abubakar a matsayin mutum mai tsananin kishin kasa, nutsuwa tare da hankali.

KARANTA KUMA: Kyawawan ɗabi'u biyar da za su inganta rayuwar aure

A nasa jawabin, babban hadimin shugaban kasa akan hulda da manema labarai, Mallam garba Shehu ya bayyana cewa, zai yi matukar kewar rashin ci gaba da mu'amala tare da shugaban na NIA a fadar ta shugaban kasa.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda 'yan jarida da kafofin watsa labarai suka soki sabon shugaban a sakamakon nadin da ya samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel