Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman jiha Kaduna sun dakatad da yajin aiki

Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman jiha Kaduna sun dakatad da yajin aiki

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya lashi takobin sai ya kori malamai 21,000

- Kungiyar malaman jihar jihar sun tafi yajin aiki sanadiyar wannan mataki

Jaridar Legit.ng Hausa ya samu rahoto daga jaridar Leadership cewa kungiyar malaman makarantun Najeriya, shiyar jihar Kaduna ta janye daga yajin aikin da suka fara. Wannan labari ya bayyana ne bayan wani taron gaggawa da sukayi.

Kungiyar Malaman sun shiga yajin aiki ne sanadiyar koran malaman makarantun firamaren jihar 21,000 da gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, yayi bayan sun fadi wata jarrabawa da ya shirya domin tantance malaman makarantun gwamnatin jihar.

KARANTA WANNAN: Wata kotu ta gurfanar da mutane biyu da laifin zambar N15m a birnin tarayya

Kungiyar ta umurci ma'aikatanta su tafi yaji aikin domin nuna rashin yardarsu da wannan abu da gwamnan yayi saboda halin kunci da rashin aikinyi da hakan zai jawo.

Kana sun ce akwai kura-kurai da dama cikin gudanan jarabawar.

Amma shi gwamnan jihar ya ce babu abinda zai hanashi koran malaman saboda basu cancanta su karantar a makarantun jihar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel