Rigima ya barke bayan wata yar shekara 19 ta bar Musulunci ta koma addinin Kirista

Rigima ya barke bayan wata yar shekara 19 ta bar Musulunci ta koma addinin Kirista

Rahoto kan ridan Misis Nabila Umar Sanda Galadima daga musulunci zuwa addinin kirista ya zamo zancen gardama a Jos, babban birnin jihar Filato.

Dalibar wacce ta kasance a shekaranta na biyu a Jami’ar Bingham, Karu, jihar Nasarawa, ta hadu da wani injiniya mai suna Simput Dafup karo na farko a Dubai.

Dafup ya kasance a hanyar dawowa Najeriya daga kasar Burtaniya, inda suka fara Magana har suka kai ga musayar lamba, ta kuma nuna ra’ayinta ga addinin kirista, Nabila ta bayyana niyyarta ga Dafup wanda ya tambayeta yanda mahaifinta Galadima Biu zai dauki al’amarin.

Nabila mai shekaru 19, ta amsa da cewa ta girma kuma ta isa yanke shawara akan al’amuranta.

Cikin rashin natsuwa, Dafup ya nemi shawarar wani malami mai suna Jerry Datim.

Yayinda yake gabatar da jawabai ga manema labarai a cibiyar NUJ a Jos a ranar Asabar, Datim ya bayyana cewa ganin abinda wannan ridan zai haifar ga dangantaka dake tsakanin kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ya yanke shawarar tattaunawa da shuwagabannin kungiyar addinin Nabila.

Datim ya ce shi da Dafup sun sadu da shugabancin JNI tare da Nabila, tare da ra’ayin kaucewa rikicin addini.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jarumar Rahama Sadau

Ya ce yayinda ake cigaba da hakan, umurni ya fito daga hukumar tsaro (DSS) sun kai farmaki gidanshi, akan matarshi, diyarshi da jariri mai watanni takwas da haihuwa, sannan suka tafi da Nabila.

Misis Dafup tace jami’an tsaron wadanda suka iso cikin motoci biyar sun kai wa mutane farmaki har da masu ketaran hanya.

Kungiyar JNI da wanda ya kai karan sun ziyarci ofishin hukumar DSS a Jos inda jami’an suka ki sauraransu, sannan suka umurcesu da su tuntubi ofishin hukumar dake Abuja don samun bayanai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel