LABARI DA DUMI-DUMI: El-Zakzaky a karon farko ya gana da manema labarai

LABARI DA DUMI-DUMI: El-Zakzaky a karon farko ya gana da manema labarai

- Sheikh El-Zakzaky a karon farko ya gana da manema labarai

- Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta aiko da hotunan shugabn IMN a yayin da yake ganawa da manema labarai

- El-Zakzaky ya bayyana cewa yana nan a raye kuma yana cikin koshin lafiya

Shugaban kungiyar 'yan Uwa Muslumi wato Islamic Movement in Nigeria (IMN) wanda da aka fi sani da Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, a karo na farko ya gana da manema labarai tun bayan da jami’an tsaro suka kama shi.

Idan dai baku manta rundunar sojin Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a garin Zaria da ke jihar Kaduna, bayan wani rikici tsakani ‘ya’yan kungiyar da sojoji wanda ta yi sanadiyar lalata gidansa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta fitar, ta ce shugaban kungiyar ya yi magana da 'yan jarida.

LABARI DA DUMI-DUMI: El-Zakzaky a karon farko ya gana da manema labarai

Shugaban kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

A sanarwar, an turo da hotunansa a yayin da yake ganawa da manema labarai.

KU KARANTA: Shugaban shi'a El-Zakzaky bai mutu ba, yana nan a raye - IMN

A wata rahoto kuma gidan talbijin na Channels ita ma ta ce Malamin ya bayyana cewa yana nan a raye kuma yana cikin koshin lafiya.

Ku biyo mu dan samun karin bayani ...

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel