2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

- Fayose ya ce har yanzu bai janye sha’awar neman shugabanci kasar ba

- Gwamnan ya ce ya dan ja birki ne saboda zaben gwamna da za a gudanar a jiharsa

- Fayose ya bayyana cewa zai sake yin nasara a kan Fayemi idan APC ta sake tsayar da shi

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose, a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu ya jaddada cewa bai janye daga neman takarar shugaban kasa wanda za’a yi a shekara ta 2019 ba, duk da cewa jam'iyyar PDP ta zartar da tikitin zuwa arewacin kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari , Fayose ya ce ya dan taka birki a kan yakin neman shugabancin ne saboda zaben gwamnan jiharsa wanda za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli, 2018, inda kuma ya ce yakin neman zabe zai fara daga tushe bayan zaben jihar.

Gwamna ya kara da cewa zai sake yin nasara a kan Dokta Kayode Fayemi idan jam’iyyar APC ta sake tsayar da shi a matsayin dan takara, inda ya ce wannan ba wai barazana bane burinsa ne.

2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose

KU KARANTA: Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

Da yake jawabi a yayin ganawa tare da malamai a makarantun firamare da sakandaren gwamnati a gidan gwamnati a Ado Ekiti, Fayose ya ce: "Ina nan daram a kan sha’awar takarar shugaban kasa, ina jira ne kawai a kammala zaben gwamnan jihar, bayan nan zan iya samun lokaci”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna ya sha kunya bayan masu sauya sheka daga PDP 4000 sun ki bayyana

Gwamna ya sha kunya bayan masu sauya sheka daga PDP 4000 sun ki bayyana

Gwamna ya sha kunya bayan masu sauya sheka daga PDP 4000 sun ki bayyana
NAIJ.com
Mailfire view pixel