Tukin motar mata a Saudiyya: Uber ta fara daukan direbobi mata aiki

Tukin motar mata a Saudiyya: Uber ta fara daukan direbobi mata aiki

- Kamfanin tukin hayar mota mai suna Uber da ke saudiyya ta fara daukan mata aikin tuki

- Wannan shi ne karo na farko da kamfanin ta dauki mata aikin tuki

- Ta fara daukan su aikin ne a shirin ta na fuskantar dage dokar hana mata tuki a watar Yuni

Kamfanin hayar mota ta Uber da ke kasar Saudiyya, ta fara daukan direbobi mata aikin tuki gabanin dage dokar hana mata tuki a watar Yuni na wanann shekarar.

Kamfanin ne ta fitar da wannan bayani a ranar Alhamis. Ta kuma ce ta fara daukan direbobin mata a reshen ta mai suna Careeem, da ke Dubai.

Kamfanin Uber ta fara shirye-shiryen daukan direbobi mata aiki a Saudiyya
Kamfanin Uber ta fara shirye-shiryen daukan direbobi mata aiki a Saudiyya

Wannan shi ne karo na farko da kamfanin za ta yi amfani da mata a matsayin direbobi. Matan kuwa da a ka kama su na tuki gabanin dage dokar hana su tukin, su na dandana kudan su ta kullen gidan yari.

DUBA WANNAN: Matasan APC suna son gwamnati ta haramta makarantun kudi

Kamfanin ta ware mintuna 90 a kullum don horas da mata game da dokokin tuki da na kan titi na kasar. Matan da ta ke horas wa tuni sun riga sun samu lasisin tukin a kasashen ketare.

Wanna dage doka da Sarki Salman ya yi da ma wasu tsauraran dokoki kan mata, yunkuri ne na Yariman Saudiyya, Mohammad Bin Salam, don zamanantar da Masarautar ta Saudiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel