Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

- Wata kotun daukaka kara ta soke zaben Mansir Aliyu Mashi (APC) dake wakiltan mazabar Mashi/Dutsi na jihar Katsina

- Ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta da ta gudanar da sabon zabe a mazabu 15

- Justis Abba Aji a shari’’arsa ya ce anyi magudin zaben a wadannan mazabu da ake Magana akai

Wata kotun daukaka kara ta dakatar da Mansir Aliyu Mashi daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake wakiltan mazabar Mashi/Dutsi na jihar Katsina.

NAIJ.com ta tattaro cewa an umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta gudanar da sabon zabe a mazabu 15 inda akayi magudin zaben.

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Kotun zabe dake Katsina ta soke zaben Mashi bayan an kawo cewa anyi magudin zaben, da kuma kwace akwatin zabe da kuma hana gudanar da zabe a wasu mazabu sannan kuma ta yi umurnin sake zabe a wadannan mazabu.

KU KARANTA KUMA: Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

Jagoran kotun daukaka karan, Kaduna, Justis Umani Abba Aji a hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu ya ce, sashin hukunci sunyi adalci a hukuncinsu, wanda ya soke zaben wanda ya zo na farko, Mansur Aliyu Mashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP

Dalilin da yasa ba zan mayar da ko sisi aljihun gwamnati ba – Tsohon gwamnan PDP

Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel