Ka saki Sambo Dasuki da El-Zakzaky yanzu – HURIWA ga Buhari

Ka saki Sambo Dasuki da El-Zakzaky yanzu – HURIWA ga Buhari

- Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta yi kira da ayi gaggawan sakin shugaban kungiyar Musulman Shia Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da Kanal Sambo Dasuki

- Kungiyar ta ce ga dukkan alamu shugaba Buhari ya manta da alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya a lokacin da ya hau mulki

- Ta yi ikirarin cewa shugaban kasar ya ce zai yi adalci ga dukkan mutane ba tare da tsoro ko alfarma ba

Wata kungiyar jama’a kuma kungiyar kare hakkin dan adam mai suna Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) ta yi Allah wadai da ci gaba da hana kungiyar Musulman Shia dake neman a saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa wanda hukumomin tsaro ke yi.

A cewar wani rahoto, kungiyar HURIWA ta yi kira da ayi gaggawan sakin tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro Kanal Sambo Dasuki.

Kungiyar ta ce ga dukkan alamu shugaba Buhari ya manta da alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya a lokacin da ya hau mulki.

Ka saki Sambo Dasuki da El-Zakzaky yanzu – HURIWA ga Buhari
Ka saki Sambo Dasuki da El-Zakzaky yanzu – HURIWA ga Buhari

Ta yi ikirarin cewa shugaban kasar ya ce zai yi adalci ga dukkan mutane ba tare da tsoro ko alfarma ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa muka biya wani tsohon shugaban kasa N40m – Sakataren gwamnatin tarayya

HURIWA ta yi ma shugaban kasa Buhari tuni ga kundin tsarin mulkin 1999 na bakwai wanda ya kasance akanta ya yi rantsuwa kafin ya hau mulki, inda ya yi rantsuwa kamar haka: Zan bi tsarin da kundin tsarin kasar tarayyan Najeriya ta gindaya, Zan yi adalci ga dukkan mutane, kamar yadda doka ta tanadar, ba tare da tsoro ko alfarma ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel