Kasashen Afirka wulakantattu ne —Inji shugaba Trump

Kasashen Afirka wulakantattu ne —Inji shugaba Trump

Rahotanni sun kawo cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi wasu kalaman wulakanci kan yan ci rani da suka fito daga kasashen Haiti, El Salvador da kuma Afirka.

A ranar Alhamis, Trump ya tambayi majalisar dokoki kan dalilin da ya sa mutanen wadannan kasashe na Afirka sunka shigo kasarsu.

Ya ce: "Me ya sa wadannan mutanen da suka fito daga wulakantattun kasashe suka shigo nan?" kamar yadda kafafen watsa labaran Amurka suka trahoto.

Wadannan kalamai, wadanda ya yi a lokacin da suke tattaunawa kan shige-da-fice, ya yi su ne kan 'yan kasashen Afirka da Haiti da kuma El Salvador.

Fadar White House ba ta musanta kalaman wulakancin da Donald Trump a kan 'yan ci-ranin ba.

KU KARANTA KUMA: Neman miji: Ko yau na samu miji da gudu zan yi aure - Rashida mai sa'a

A makonnin baya bayan nan, gwamnatin Trump na ta kokarin ganin ta takaita iyalan 'yan ci-ranin da ke zaune a kasar da za a iya barin su su shiga Amurka, kuma ta dauki matakin ganin ta soke izinin zaman mutane da dama a kasar.

Kalaman wulakancin da Mista Trump ya yi sun faru ne a lokacin da 'yan majalisar daga jam'iyyun kasar suka kai masa ziyara ranar Alhamis domin gabatar masa da kudirin dokar shige-da-fice wanda suka amince da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel