Kifewan jirgin ruwa yayi sanadiyar bacewar mutane 100 a Libya - Rundunar sojin ruwa

Kifewan jirgin ruwa yayi sanadiyar bacewar mutane 100 a Libya - Rundunar sojin ruwa

- Rundunar sojojin ruwa na kasar Libya,ta ce yan gudun hijira guda 100 sun bace a cikin ruwa yayin da jirgin da ya debo su ya kife

-Kungiyar kula da yan gudun hijira na Duniya ta ce gudun hijira 2,832 suka mutu a shekara 2017 a Arewacin Afrika

Rundunar sojojin ruwa na kasar Libya, ta ce yan guduna hijira guda 100 sun bace yayin da jirgin ruwan da ya dauko su ya kife a tekun Libya.

Jami’an tsaron tekun Libya sun ceci mutane 17 a lokacin da jirgin ruwan ya nutse a garin al-Khoms dake kudancin kasar Libya.

Kifewan jirgin ruwa yayi sanadiyar bacewar mutane 100 a Libya - Rundunar sojin ruwa
Kifewan jirgin ruwa yayi sanadiyar bacewar mutane 100 a Libya - Rundunar sojin ruwa

Wadanda suka rayu sun makale ne a jiKin jirgin da ya kife kafin aka ceci rayuwan su.

KU KARANTA : Yan kwangila suna bin gwamnatin tarayya bashin naira triliyan N2.8trn - Fashola

“Ammayan gudun hijira 90 zuwa 100 sun bace a cikin tekun Libya inji rundunar sojin ruwan kasar Libya.

Kungiyar kula da yan gudun hijira na Duniya ta ce sama da yan gudun hijira 2,832 suka mutu a shekara 2017 a Arewacin Afrika a lokacin da suke kokarin zuwa kasar Italiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel