Da duminsa: Wata kotun tarayya ta soke hukuncin dakatarwar da jam'iyyar PDP ta yiwa wani Sanata

Da duminsa: Wata kotun tarayya ta soke hukuncin dakatarwar da jam'iyyar PDP ta yiwa wani Sanata

- Wata babban kotun a Abuja ta share wa Sanata Kashamu hawaye

- Kotun ta soke hukuncin dakatarwa da jam'iyyar ta yi wa Sanatan mai wakiltan yankin Ogun ta gabas

- Kotun har ila yau ta dakatar da mahukuntan jam'iyyar daga daukan wani matakin ladabtarwa a kan sa

Wata babban kotun garin Abuja ta soke dakatarwar da jam'iyyar PDP ta yi wa Sanata mai wakiltan yankin Ogun ta gabas, Buruji Kashamu daga jami'iyyar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kotun kuma tayi hani ga mahukuntan jam'iyyar daga daukan ko wane matakin ladabtarwa a kan Sanatan.

Alkali Valentine Ashi na babban kotun birnin Tarayya Abuja ne ya da ke Apo ne ya zartar da wannan hukuncin a yau Talata 9 ga watan Janairu.

Da duminsa: Babban Kotun Tarayyah tayi watsi da dakatarwar da aka yi wa Buruji Kashamu daga PDP
Da duminsa: Babban Kotun Tarayyah tayi watsi da dakatarwar da aka yi wa Buruji Kashamu daga PDP

KU KARANTA: An kamalla hada sakamakon jarabawar mutane 43,000 masu neman aikin malanta a jihar Kaduna - El-Rufa'i

Kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ne ta dakatar da Kashamu sa'o'i kadan kafin fara zaben jam'iyyar na shekara-shekara da aka yi a ranar 9 ga watan Disamba.

Nan take Kashamu ya garzaya zuwa kotu inda ya kai karar kwamitin gudanarwar jam'iyyar amma bai samu daman hallartan taron ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel