Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki - Jafar jafar

Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki - Jafar jafar

- Shugaba Buhari ya taba cewa bai zai yi tazarce ba idan ya ci zabe

- Buhari ya ce ba zai yi tazarci ba saboda shekarun sa sun fara tafiya kuma yana tsufa

A wata hira da, Theophilus Abbah, yayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a watan Faburairu na shekara 2011 ya tambaye shi cewa mai yasa yace ba zai yi tazarce ba idan ya ci zabe?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaba da amsa da cewa, shekarun sa sun fara tafiya kuma yana tsufa. Saboda haka Idan yanzu ya ci zabe bayan ya kammala wa’adi daya akan mulki shekarun sa za su kai 73.

Theophilus Abbah ya kara tambayar shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa, idan yace zabe menene zai gagauta yi a gwamnatin sa ?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace masa akwai abubuwa guda biyu da su ke ci masa tuwo a kwarya game da al’amarin Najeriya wanda ya kunshi rashin tsaro da rashin wutar lanyarki.

shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bai kamata yan Najeriya su rika yawo a cikin kasar su, suna tsoron za a iya sace su a kowani lokaci.

KU KARANTA : DPR ta yi wa masu motoci kyautar litar mai 300 daga gidan man fetur din da ta rufe

Mutane sun gina gidaje da biliyoyin kudi a Najeriya amma basa iya zama a ciki, saboda rashin tsaro.

Na biyu shine, ya zama dole a farfado fannin wutar lantarki a kasar, saboda yan Najeriya su samu saukin wajen yin kasuwanci a kasar.

Sauran shine gyara hanyoyin da inganta tashoshin ruwa da hanyoyin jirgin kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel