Hajjin bana: Saudiyya ta sake baiwa Najeriya kujeru 95,000

Hajjin bana: Saudiyya ta sake baiwa Najeriya kujeru 95,000

Hukumar aikin hajji ta kasar Saudiya ta yi tanadin kujeru 95,000 ga maniyyatan Najeriya da zasu gudanar da aikin hajjin su a bana, wannan shine adadin kujeru da gwamnatin kasar ta baiwa Najeriya a shekarar da ta gabata.

Mallam Adamu Abdullahi, kakakin hukumar jin dadin Alhazai ta kasa wato NAHCON, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labaran karshen mako na kamfanin jaridar Leadership a birnin tarayya.

Yake cewa, wannan hukuncin yazo ne da sanadin yarjejeniyar da ta wakana a yayin ganawa da hukumomin biyu suka aiwatar a kasa mai tsarki.

Adamu ya ci gaba da cewa, ganawar tazo domin fara shirye-shirye na gudanar da aikin hajjin bana, inda ganawar ta kunshi tawagar kasar Saudiya da ministan Hajji da Umarah, Dakta Muhammad Bin Tahir Bentenand ya jagoranta. Sai kuma karamar ministan harkokin kasashen ketare, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ta jagoranci tawagar wakilan Najeriya.

Maniyyatan aikin hajji
Maniyyatan aikin hajji

Tawagar 'yan Najeriya ta kuma kunshi shugaban hukumar Alhazai ta kasa baki daya, Barrister Abdullah Mukhtar Muhammad.

Legit.ng ta fahimci cewa, wakilan Najeriya sun yabawa kwazon da kasar Saudiya ta yi wajen saukar baki na mahajjata sama da miliyan 2 da tayi a shekarar da ta gabata ba tare da samun wata tangarda ba.

Wakilan na Najeriya sun kuma jajinta dangane da hare-haren ta'addanci na kwana-kwanan nan da suka afku a kasar, inda suka ce Najeriya tana yakar duk wani nau'i na ta'addanci.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya tana da zabi uku akan N145 na farashin man fetur

Tawagar Najeriya ta kuma sake jaddawa hukumar kasar Saudiya dangane da karancin bukkoki a Mina da mahajjatan Najeriya suka fuskanta a yayin gudanar da aikin hajji na bara, inda ta mika kokon ta na bara domin a inganta jin dadin alhazanta a yayin gudanar da aikin hajji na bana.

A nasa jawabin kuma, ministan na Saudiya ya yabawa hukumar aikin hajji ta Najeriya dangane da irin kwazon da ta nuna a aikin hajji na bara, wanda hakan ya sanya kasar ta samu karin kima da mutunci a idon duniya.

Ministan ya kuma shaidawa wakilan na Najeriya cewa, akwai manufa da kasar Saudiya take da ita na ingantawa tare da sake bunkasa gine-gine a Mina daga yanzu zuwa shekarar 2030.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel