Takaitaccen tarihin bakar fatar da yayi fice a duniya ta fuskar kudi a 2017

Takaitaccen tarihin bakar fatar da yayi fice a duniya ta fuskar kudi a 2017

Babu tantama kididdigar mujallar Forbes mai da zakule-zakulen bincike a duniya ta bayyana cewa, shahararren dan kasuwar nan na Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, shine bakar fatar da yayi fice ta fuskar nauyi da kuma zurfin aljihu a duniya a shekarar 2017.

Legit.ng ta fahimci, Aliko Dangote ya taka sahun shahararrun masu kudin duniya irin su Bill Gates, Warren Buffet da kuma Jeff Bezos, inda kimarsa ta kudi ta taka matakin biliyan domin kuwa zancen miliyan na kananan kwari ne a yanzu.

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote

Akwai sauran bakaken fata da nauyin aljihunsu ya sanya suka shiga cikin kididdigar ta mujallar Forbes da suka hadar da; Tony Elumelu, Mo Ibrahim, Isabel Dos Santos, Theophilus Danjuma, Patrice Motsepe, Folorunsho Alakija, Oprah Winfrey, Mike Adenuga da kuma Mohammed Al-Amoudi.

  • Dangote cikakken bahaushe ne kuma musulmi da aka haifi shi a ranar 10 ga watan Afrilun 1957 a jihar Kano.
  • Ya taso a cikin dangi masu yalwar arzikin. Kakansa, Alhaji Alhassan Dantata shine mutumin da ya kere kowa kudi a shekarar 1955 a nahiyyar Afirka.
  • Ya karatunsa a jami'ar Al-Azhar ta Cairo dake kasar Masar a fannin nazarin kasuwanci.
  • Yana zaune a jihar Legas da 'ya'yansa hudu, uku mata (Halima, Mariya da Fatima), sai kuma wani da da yake rikon sa (Abdurrahman Fasasi).
  • Dangote yayi aure har sau biyu sai dai sun rabu da matarsa da farko. Har yanzu wasu suna masa kallon gauro sakamakon rashin sanin kowace matarsa ta yanzu.
  • Aliko Dangote mutum ne mai kyauta, domin kuwa a shekarar 2003 ya bayar da $2m wajen kamfe din tsohon shugaban kasa Obasanjo.
  • Ya kuma bayar da taimakin $500, 000 wajen ginin babban masallacin Najeriya dake Abuja da kuma wata $2m da ya bayar wajen babbago da dakin nazari na shugaban kasa.
  • A shekarar 2014 kuma, ya bayar da tallafin N150m domin yakar cutar Ebola.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel