Wahalar fetir: Labari da hotunan yadda ta kasance tsakanin Baru da 'yan majalisa

Wahalar fetir: Labari da hotunan yadda ta kasance tsakanin Baru da 'yan majalisa

- Baru ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai a yau

- Ya bayyana cewar jita-jitar karin farashin man fetir ce usulin wahalar man a kasa baki daya

- Ya ce yanzu haka babu dogwayen layukan ababen hawa a gidajen man fetir a Najeriya

Shugaban kamfanin man fetir na kasa (NNPC), Maikanti Baru, ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai domin amsa tambayoyi a kan matsalar wahalar man fetir da ta jefe 'yan Najeriya cikin kunci yayin shagulgulan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Wahalar fetir: Labari da hotunan yadda ta kasance tsakanin Baru da 'yan majalisa
Wani bangare na 'yan majalisar dattijai yayin zaman kwamitin

Majalisar Dattijai ta katse hutun da take yi tare da aike sammaci ga Baru domin ya bayyana a gaban kwamitinta na man fetir domin fayyace masu makasudin faruwar wahalar man da kuma matakan da hukumar NNPC ta dauka domin shawo kan matsalar.

Baru ya bayyanawa kwamitin majalisar cewar, tun asali, jita-jitar karin farashin man fetir ce ta fara haddasa matsalar karancin man fetir din.

Wahalar fetir: Labari da hotunan yadda ta kasance tsakanin Baru da 'yan majalisa
Baru ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai

A cewar Baru "Akwai wadataccen man fetir a matatu da ma'adanan man fetir dake fadin kasar nan. Muna da kimanin lita biliyan 1.9 na man fetir da zata iya wadata Najeriya da mai na tsawon kwanaki 53. Amma bayan fara yada jita-jitar karin farashin man fetir sai 'yan kasuwa suka fara boye man da suke da shi. Sai cunkuson ababen hawa ya fara bayyana a gidajen man fetir dake fadin kasar nan."

DUBA WANNAN: Yadda wahalar man fetir ta shafi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara

Baru ya kara da cewar dillala man fetir sai suka shiga boye man da suke da shi tare da karkatar da wanda suke siya daga hannun hukumar NNPC.

Da yake bayanin irin matakan da hukumar NNPC ta dauka domin shawo kan matsalar, Baru, ya ce sun kirkiri matakai domin kawo karshen wahalar fetir din da 'yan kasuwa suka kirkira ta hanyar kafa kwamitin sa ido da zai tabbatar an daina karkatar da fetir ko boye shi, kara adadin man da ake fitarwa kowacce rana, sanya takunkumi ga masu boye man ko sayarwa a fiye da farashin gwamnati, da sauransu.

Wahalar fetir: Labari da hotunan yadda ta kasance tsakanin Baru da 'yan majalisa
Maikanti Baru da Ibe Kachikwu yayin zaman kwamitin majalisar dattijai

A karshen jawabinsa, Baru, ya ce yanzu dogwayen layukan ababen hawa a gidajen Mai dake fadin kasar nan ya bace sakamakon matakan da suka dauka. Kazalika ya ce hukumar NNPC ta dauki karin wasu matakan domin ganin irin matsalar bata sake afkuwa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel