Rikita-Rikita: Kungiyar Real Madrid ta shiga tsomomuwa

Rikita-Rikita: Kungiyar Real Madrid ta shiga tsomomuwa

Dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema zai yi jinya, sakamakon raunin da ya ji a wasan hamayya da Barcelona wanda ake yi wa lakabi da El Clasico.

Real ba ta bayyana ranar da Benzema zai dawo fagen tamaula ba, bisa raunin da ya yi a kafarsa ta hagu ba.

Rikita-Rikita: Kungiyar Real Madrid ta shiga tsomomuwa
Rikita-Rikita: Kungiyar Real Madrid ta shiga tsomomuwa

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa ana rade-radin cewar dan kwallon ba zai buga wasan Copa del Rey da Real za ta yi da Numancia gida da waje da karawa da Celta Vigo a gasar La Liga da watakila fafatawa da Villarreal da kuma Deportivo La Coruna ba.

Benzema bai halarci atisayen da Madrid ta fara a ranar Asabar ba, sai da likitocin kungiyar sun duba girman raunin da ya yi a ranar 23 ga watan Disamba.

Real Madrid wadda ta ci kofi biyar a 2017, tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu da Paris St Germain a gasar Zakarun Turai a watan Fabrairu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel