Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da Sheikh Abdulrahman As-Sudais

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da Sheikh Abdulrahman As-Sudais

Abdulrahman Ibn Abdul-Aziz as-Sudais yana daga cikin manya-manyan malaman addinan musulunci wanda suka fara yi wa addini hidima tun suna yara. Babban malamin ne ya lashe kyautar karatun Al-Qurani mai girma na duniya da aka gudanar a Dubai a shekerar 2005.

Yana kuma bayar da gudunmawa a kan al'amura daban-daban da suka hada da da'awah, bayar da fatawa, samar da zaman lafiya da cigaba tsakanin musulmai da abokanan zaman su.

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da Sheikh Abdulrahman As-Sudais
Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da Sheikh Abdulrahman As-Sudais

Ga dai wasu mahimman ababe da ya kamata mai karatu ya sani game da Shaihin Malamin.

1) An haife Abdulrahman Ibn Abdul-Aziz as-Sudais a babban birnin Saudiyya wato Riyadh a 1960 kuma shi dan kabilar Anza ne.

2) Ya haddace Al-Kura'ani mai girma yana yaro kankani dan shekaru 12 a duniya kacal.

3) Ya kammala digirin sa na farko a fannin Shari'ar musulunci a Jami'ar Musulunci na Imam Muhammad bin Saud da ke Riyadth a 1983. Ya kuma yi digiri na 2 da na 3 duk dai a fannin na addinin musulunci a 1995.

KU KARANTA: Dubi kyawawan hotunan gidajen da Hukumar Sojin Saman Najeriya ta gina wa hafsoshin ta a Benin

4) Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Farfesa a Jami'ar Riyadth da kuma Jami'ar Umm ul Qura

5) An zabe shi a matsayin limamin babban masallacin Saudiyya yana da shekaru 22 a duniya, ya kuma yi hudubar sa ta farko ne a watan Yuli na 1984.

6) An shekarar 2012, an nada shi a matsayin Minister kuma shugaban gudanarwa na masallatan garuruwan Makka da Madina.

Allah ya karba ayyukan sa kuma ya saka masa da gidan Aljanna Firdausi. Amin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel