Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya

Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya

- Mun kawo maku manyan abubuwan da su ka faru a bana

- Daga ciki dai akwai rashin lafiyar Shugaban Kasa Buhari

- Akwai kuma sauya sheka da Atiku yayi daga APC zuwa PDP

Mun kawo maku jerin wasu abubuwa na fice da su ka auku a shekarar bana watau 2017 da za a dade ba a manta da su ba a tarihin siyasar kasar. Jaridar The Cable ta gutsuro da dama daga ciki:

Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya
Shugaba Buhari yayi doguwar jinya a Kasar waje

1. Rashin lafiyar Shugaban Kasa Buhari

A bana ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ta fama da rashin lafiya a Birnin Landan har wasu ke tunanin ya cika ko kuma ba zai yi rai ba.

KU KARANTA: Tarihin Sarakunan Kasar Zazzau a Tarihin Hausa

2. Sallamar Sakataren Gwamnatin Tarayya

A wannan shekara ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Sakataren Gwamnatin sa Babachir David Lawal bayan ya dakatar da shi na tsawon lokaci. An kuma sallami Shugaban Hukumar NIA Ayo Oke bayan wani bincike.

Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya
Buhari ya kori Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir

3. Shari’ar Shugaban Majalisar Dattawa

Haka kuma a bana Kotu ta wanke zargin da ke kan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki inda aka yi watsi da karar. Yanzu haka dai an kuma dawo da maganar Kotu. Majalisar ta shiga cikin rikici iri-iri bayan ta dakatar da wasu ‘Ya ‘yan ta.

Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya
Saraki yayi nasara a Kotu na zargin boye kadarorin sa

4. Yunkurin yi wa Sanata kiranye

An kai an koma wajen dakatar da Sanatan Kogi Dino Melaye daga Majalisar Dattawan Kasar. Har yanzu dai maganar ta nan a Kotun daukaka kara.

Fagen siyasa: Manyan abubuwan da su ka faru bana a Najeriya
Atiku ya sulale daga APC zuwa inda ya fito

5. Kai-komo da sauye-sauye a Jam’iyyar adawa

A karshen shekarar nan ne Jam’iyyar PDP tayi kamu inda Atiku Abubakar ya dawo bayan ya bar APC. Jam’iyyar tayi ta rikici a Kotu wanda bayan nan aka yi nasara har aka kai ga zaben Shugabanni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel