Rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja

Rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja

- Rahotanni sun bayyana cewar wani rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja

- Rikicin yana da nasaba da kabilanci

- An alakanta wasu matsafa da kunna wutar rikicin

Wani rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja bayan da wasu da ake zargin 'yan kungiyar matsafa ne suka kai hari garin ranar Lahadi da daddare.

Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum guda da kone kusan rabin kasuwar Bwari.

Rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja
Rikici ya barke a garin Bwari dake Abuja

Ance rikicin ya yi kamar ya kwanta a ranar Lahadin, amma sai yau ya dawo danye. Rikicin dai an bayyana cewar tsakanin kabilar Gbagi (Gwari) da Hausawa.

Kabilar Igbo da Hausawa ne mafi yawan 'yan kasuwar da aka kone..

DUBA WANNAN: Gudun rayuwa a cikin bukka ya saka 'yan Najeriya ke tsoron komawa Afrika - Donald Trump

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da barkewar rikicin tare da bayyana cewar tuni ta baza jam'ianta a garin na Bwari domin kwantar da rikicin.

Saidai hukumar bata bayyana adadin mutanen da suka mutu ko samun raunuka ba. Hakazalika bata bayyana dalilin barkewar rikicin ba.

Wasu mazauna garin Bwari sun fadawa gidan Rediyon BBC cewar duk kabilun suna zaune lafiya da juna kafin barkewar rikicin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel