Labari mai dadi: Sababbin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna sun iso

Labari mai dadi: Sababbin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna sun iso

Rahotanni daga Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jiragen kasa da hukumar jiragen kasa (NRC) ta siya don aikin jigilar Abuja-Kaduna sun iso Abuja a karshen makon da ya gabata.

Daga cikin jirage goma da ake sa rai, hudu sun isa Abuja.

Majiyarmu, wanda ya ziyarci tashar jirgin kasan Idu Abuja a karshen mako da ya gabata, ya rahoto cewa an soma sauke injin jirgin kasa.

An soma kafa jiragen kasan don daurasu bisa hanya.

Labari mai dadi: Sababbin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna sun iso
Labari mai dadi: Sababbin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna sun iso

Mai sadarwa a hukumar NRC, Mista Pacal Nnorti ya fada wa majiyarmu a wurin cewa sauran jiragen shida zasu iso nan bada da dadewa ba.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 9 da ba’a sani ba game da shugaba Buhari

Yace daga cikin jiragen goma, shida sun kasance na tattalin arziki, biyu na gudanarwa sannan biyu da suka rage zasu kasance na daukan kaya.

Hukumar NRC tana shirye shiryen kaddamar da jirage biyu a ranar 15 ga watan Janairu, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel