Wani saurayi ya murkushe kanwar sa a jihar Katsina

Wani saurayi ya murkushe kanwar sa a jihar Katsina

Wani saurayi mai shekaru 18, Sa'idu Abdullahi, ya gurfana a gaban babbar kotun majistire dake jihar Katsina bisa laifin zakkewa ƙanwarsa 'yar shekaru 8 a duniya.

An tuhumi Abdullahi wanda dalibin aji daya ne a daya daga cikin makarantun sakandire na jihar, da laifin ketawa ƙanwarsa haddinta a gidan iyayen su dake unguwar Jabango a jihar ta Katsina.

Wani saurayi ya murkushe kanwar sa a jihar Katsina
Wani saurayi ya murkushe kanwar sa a jihar Katsina

Kotun tana zargin Abdullahi da laifin saduwa da ƙanwar sa da babu aure a tsakanin su, wanda hakan ya sabawa sashe na 390 na tsarin dokar kasa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya tayi amai ta lashe akan $1bn data ware na yakar ta'addancin Boko Haram

Alkaliyar kotun Fadila Dikka, ta bayar da belin wanda ake zargi tare da ba shi umarnin bayyana a gabanta a ranar 14 ga watan Fabrairu, na shekarar 2018 domin sauraron karar.

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'in dan sanda Sajen Sani Rabi'u, shine ya damko kugun Abdullahi bayan ya yaudari ƙanwar tasa zuwa wani kango dake daura da kamfanin kera rodi.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel