Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta hararowa mata ma'aurata bankayen dake cikin tsafta a gidajen aure

Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta hararowa mata ma'aurata bankayen dake cikin tsafta a gidajen aure

Fitacciyar jarumar nan ta shirin fina-finai na wasan hausa Mansura Isah, ta gargadi mata musamman ma'aurata akan tsaftace jikin su da kuma muhallan su a gidajen su na aure.

Mansura wadda uwargida ce ga shahararren jarumin nan na Kannywood, Sani Musa Danja, tayi wannan jan hankali ne a wata ganawa da 'yan jarida na kamfanin Tozali, inda take baiwa mata shawarwari da kuma hararo musa amfanin tsafta a gidajen su na aure.

Mansura Isah tare da mai gidanta Sani Musa Danja
Mansura Isah tare da mai gidanta Sani Musa Danja

Jarumar ta nemi mata da su rika tsaftace jikin su wanda aikata hakan zai kara musu dankon soyayya tare da habakar sha'awar mazajen su a gare su.

KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Yadda nayi artabu da masu garkuwa da mutane - Al-amin Buhari

Ta kuma nemi matan da su rungumi tsaftace muhallansu tare da wuraren su na zama tare da yin kwalliya da kuma ado ga mazajen su wajen yin amfani da kayan shafe-shafe kamar turare na jiki da na muhallai da su kara dankon soyayya a zukatan mazajen na su.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel