‘Yar Arewa ta kai kololuwar matsayi a aikin Sojan ruwa a Najeriya

‘Yar Arewa ta kai kololuwar matsayi a aikin Sojan ruwa a Najeriya

- Wata Mata daga Arewacin Najeriya ta zama Janar din Sojan ruwa

- A tarihin Kasar ba a taba samun wanda ta kai wannan mataki ba

- Jamila Malafa ta shiga aikin Soja ne tun shekaru 27 da su wuce

Yayin da ku ke jin labari wani Ango ya sha da kyar bayan Amaryar sa ta kusa kashe sa da makami. Mun kuma samu labari mai dadi na wata Sojar Najeriya ta farko daga Arewa ta kai matakin Janar kwanan nan.

‘Yar Arewa ta kai kololuwar matsayi a aikin Sojan ruwa a Najeriya
Wata ‘Yar Arewa ta kai matsayin Janar a aikin Soja

A karon farko an samu Sojar da ta fito daga Arewa da ta kai mataki na kusa da kololuwa a aikin Sojan ruwa. Kyaftin Jamila Malafa ce ta kai matakin Komodo kwanan nan wanda ya ke tamkar Birgediya Janar a gidan Sojan Kasa.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya kara wa'adin su Buratai da Olanishakan

Jaridar Daily Trust tace a kan Komodo Jamila ne aka taba samun wata mace daga Arewacin Najeriya da ta kai matsayin mai taurora daya a khali a kaf tarihin Kasar, Ko a matan Kudu ma dai kadan ne su ka kai wannan matsayi.

Wani babban Jami’in Sojin ruwa na kasar Admiral Henry Babalola ya yabawa Jamila Malafa wanda ta fito daga Jihar Adamawa ya kuma nemi ayi koyi da ita. Jamila ta shiga Soja ne a 1988 inda aka kaddamar da ita a 1990.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel