Sabon rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a jihar Binuwe

Sabon rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a jihar Binuwe

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da barkewar wani sabon rikicin kabilanci a tsakanin mazauna kauyen OGobia dake a karamar hukumar Otukpo ta jihar Binuwe inda tuni har anyi asarar rayukan mutane 4.

Majiyar mu dai ta Dailytrust ta ruwaito cewa a kwanan baya ma dai 14 ga watan Satumbar da ta gabata an samu mutuwar wani tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a jihar, Manjo Laurence Ugbor da wasu mutane 5 din ciki hadda tsohon jami'in dan sanda sakamakon wani rikicin kabilancin a karamar hukumar.

Sabon rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a jihar Binuwe

Sabon rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a jihar Binuwe

NAIJ.com haka zalika ta samu dai cewa tun farko a cikin watan Fabrairu ma na shekarar da ta wuce rayuka da dama sun salwanta a kauyukan Ondo da Ogobia biyo bayan wani rikici kan kasar noma da daga baya ya rikide ya koma rikicin siyaysa.

Haka ma dai mai magana da yawun jami'an yan sandan jihar mai suna Moses Joel Yamu ya tabbatar da aukuwar rikicin inda kuma ya bayyana cewa mutum 3 ne suka mutu a ranar da rikicin ya faru watau Asabar yayin da na hudun ya mutu jiya Lahadi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel