Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

- Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

- Wannan shirin za ta ci gaba wanda a kashi na farko aka fara da jihohin Sakkwato, Kaduna, Kebbi da kuma Kano

- Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin dadin su da godiya ga sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta tallafawa mata 100 masu kananan sana'o'i da jari a garin Sakkwato domin taimaka musu wajen kara zama masu dogaro da kai.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Hon. Aliyu Sani Madakin-Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai a jawabinsa a lokacin bikin kaddamar da bayar da kyautar kudin ya ce karfafawa musamman mata da matasa a fannin sana'o'i na daya daga cikin manufofin akidar Kwankwasiyya.

Ya ce Akidar Kwankwasiyya Akida ce wadda ke kokari domin tabbatar da mulkin gaskiya da adalci tare da tallafawa al’umma marasa galihu da 'ya'yan talakawa a fadin kasar.

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

"Akalla mata 100 ne aka zaba wadanda suka caccanta da tallafin naira 10, 000. Wannan shirin dai za ta ci gaba wanda a kashi na farko aka fara da Jihohin Sakkwato, Kaduna, Kebbi da kuma Kano”, inji shi.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta kafa kahon zuka akan Dala Biliyan 1 da gwamnatin APC ta ware don yakar Boko Haram

A jawabin Hon. Malami Bajare, jagoran Kwankwasiyya na jihar Sakkwato, ya bayyana cewa Akidar Kwankwasiyya ta samu gagarumar karbuwa a Sakkwato da wajen ta a dalilin gamsuwa da kyawawan manufofi da kudurorin alheri da Kwankwasiyya take da shi ga al'ummar kasar nan.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin dadin su da godiya ga tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan tallafin da ya ba su tare da alkawalin amfani da kudin yadda ya kamata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel