Dandalin Kannywood: Yadda nayi artabu da masu garkuwa da mutane - Al-amin Buhari

Dandalin Kannywood: Yadda nayi artabu da masu garkuwa da mutane - Al-amin Buhari

A sakamakon garkuwa tare da neman kudin fansar fitaccen jarumin nan na wasan Hausa, Al-amin Buhari, manema labari na kamfanin jaridar Daily Trust sun samu ganawa da shi inda ya fayyace musu zare da abawa kan yadda ta kasance tun daga fari.

Jarumin dai ya bayyana cewa wannan lamari ya afku ne da misalin karfe 5:00 na Yammacin ranar Lahadi 3 ga watan Dasumba, a daidai lokacin da suke kan hanyar su daga birnin tarayya zuwa birnin Jos inda yake zama. Yake cewa su uku sun kasance a cikin mota tare da jarumin nan, Abdullahi Karkuzu, sai kuma mai daukar hoto da bidiyo na kamfanin 3SP Films Production, Salahuddeen.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokaci da suka wuce garin Keffi dake karkashin jihar Nasarrawa bayan sun wuce garin Garaku. Sai kwatsam ba su yi aune ba suka hango wani abu tamkarhatsarin motoci tare da mutane wasu a kwan-kwance, wata mata da jaririn kuma farfajiyar wajen duk jina-jina. Hakan ya sanya suka rage gudun motar su wanda isar su ke da wuya sai ga wasu mutane rike da bindigu kuma sanye da kayen jami'an tsaro na 'yan sanda. Inda suka tsayar da su kuma suka ce su fito daga motar, cikin gaggawa suka fito ba tare da wani dogon nazari ba.

Buhari ya ci gaba da cewa, sun sanya muku fito daga motar tare da bamu umarnin mu kwanta a kar da karbe mana wayoyin mu na salula da kuma Naira 62, 000 dake aljihuna da agogo na na daurawa a hannu.

Bayan kimanin mintuna uku, sai suka umarce ni da Salahudden akan mu tsahi tsaye da angiza keyar mu cikin daji, inda suka bar Karkuzu a cikin motar da gargadin sa akan ya tsahirta sai sun gama aikin su.

Jarumi Al-amin Buhari
Jarumi Al-amin Buhari

A yayin da muke tafe sai Salahu ya kawo shawarar mu arce, na ce a'a idan mun gudu ina za mu shiga baya ganin cewar a cikin daji muke. Na shawarce akan ya ci gaba rokon Rabbani ya kubutar damu. Salahu dai ya ci gaba da angiza mu akan mu arce, sai kurum da dauki shawarar sa inda ya bi hagu ni kuma nayi dama. Kafin muyi wani dogon zango wasu mutane biyu suka datse Salahu kuma suka lakada masa duka da kan bindigar su. Ban yi aune ba wanda ke bi na a baya yace in har ban tsaya zai dadara min harsashi sai kuwa na dakata kuma nayi malamale a kasa, ya sake umarta ta akan na tashi tsaye kuma mu ci gaba da tafiya.

Mun yi tafiya ta kusan awanni 9, sai suka bani damar yin Sallah ta Magariba da kuma Isha, kasancewar su salloli ne masu karatun bayyane sai daya daga cikin 'yan ta'dda tunda ni Ustazu ne nayi musu addu'a akan su daina wannan ta'asa domin su ma ba a son ran su suke aikatawa ba.

Haka muka wayi gari, inda budewar rana ke da wuya suka rufe mani idanu har wani daren ba tare da bani ci ko sha ba sai dai sun bani damar yin salloli na.

A cikin wannan dare ne suka nemi da na basu lambar wani da nasan zai iya biyan kudin fansa ta. Sai kuwa na bayar da lambar aboki na Alhaji Sani, suka fara tattaunawa da shi kuma suke nemi fansar Naira miliyan 15. Daga bisani suka rage adadin kudi zuwa Naira miliyan 10. Na fada musu cewa bani da wani kudi a tare dani. Wanda a yayin da suka ci gaba da tattaunawa da Alhaji Sani suka amince akan karbar fansar Naira 500, 000.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP ta kafa kahon zuka akan Dala Biliyan 1 da gwamnatin APC ta ware don yakar Boko Haram

Na nemi abokina da ya sayar da motar dana ke hawa, wanda kashe garin ranar Litinin da misalin karfe 12: 00 na ranar, Alhaji Sani ya kawo musu kudaden inda suka aika daya daga cikin su karbo kudin kuma ya tabbatar musu kudin sun cika, sai kuwa suka ce na kama gabana tare da yi mani addu'ar Allah ya tsare.

Samun labarin halin da na ke ciki ya sanya iyali na cikin hali na tashin hankali, wanda Alhaji Sani ya lallashe akan su ci gaba da yi mani addu'a komai zai wuce, kuma cikin ikon Mai duka yanzu ya zama tarihi.

'Yan jarida sun sake tambayar Al-amin shin ko yana da aniyyar yin wani shirin fim akan yadda ake garkuwa da mutane da kuma yadda za a magance shi? Budar bakin sa yace, a yayin da yake tsare a wajen 'yan ta'adda bayan da suka fahimci sana'ar wasan kwaikwayo nake, sai muka fara tattaunawa inda suka nemi da na shirya fim akan abinda ya faru a gare ni da cewar za su kalli shirin domin ya tunasar musu da aikata wannan shu'umanci, sai dai a halin yanzu bani da shiri akan aiwatar da hakan.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel