Akwai yiwuwar dakatar da kasar Spain daga karawa a gasar kofin duniya ta 2018 - FIFA

Akwai yiwuwar dakatar da kasar Spain daga karawa a gasar kofin duniya ta 2018 - FIFA

Akwai yiwuwar kasar Spain ba zata samu damar karawa a gasar kofin duniya ba da za a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018 mai gabatowa .

NAIJ.com ta kawo muku wannan rahoton ne da sanadin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, inda ta bayyana hakan a sakamakon katsalandan da hukumar kwallon kafa ta kasar Spain take yi mata a zaben shugabanta.

Rahotanni daga jaridar El Pais ta ruwaito cewa, hukumar FIFA ta aika wasika ga hukumar kwallon kafa ta kasar Spain wato RFEF (Royal Spanish Football Federation), inda tayi mata barazanar dakatar da kasar daga samun damar karawa a gasar kofin duniya muddin ta yi gaban kan ta wajen zaben sabon shugaban ta.

Murnar nasarar gasar kofin duniya da kasar Spain tayi a shekarar 2010

Murnar nasarar gasar kofin duniya da kasar Spain tayi a shekarar 2010

Juan Larea shi ke rike da hukumar RFEF a halin yanzu, inda tsohon shugabanta Angel Maria Villar yayi murabus a sakamakon tuhumar sa da ake yi da aikata laifukan rashawa.

KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur zata fada yajin aiki gadan-gadan

Akwai yiwuwar hukunta kasar Spain kamar yadda kasar Kuwait ke fuskantar makamancin wannan hukunci a sakamakon katsalandan da hukumomin kwallon kafa na kasar suka yiwa FIFA.

Idan mai karatu bai sha'afa ba a baya cikin shekarar 2010, kasar Spain ta fuskanci makamanciyar wannan barazana a lokacin shugaban FIFA Sepp Blatter, inda shaidu da kididdigar bincike bata kamata da wani laifi ba.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - In ji Kawu Baraje

Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - In ji Kawu Baraje

Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - In ji Kawu Baraje
NAIJ.com
Mailfire view pixel