Shirye-shirye na hawan daban bikin cikar Kaduna shekaru 100 da kafuwa

Shirye-shirye na hawan daban bikin cikar Kaduna shekaru 100 da kafuwa

- Sarkin Gombe ya kammala duk wani Shirye-shirye na hawan daban bikin cikar Kaduna shekaru 100 da kafuwa

- Za a gudanar da hawan daban ne a yau Asabar a dandalin Murtala Square da ke Kaduna

- An Kafa jihar kaduna a shekara ta 1917 zamanin gwamna ‘Lord Lugard

Mai martaba sarkin Gombe, (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III, ya kammala dukkanin shirye shiryen da ya kamata don kayatar da masu kallo a filin hawan daba mai tarihi wanda za a yi a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba a garin Kaduna.

Za a gudanar da wannan gagarumin hawan daba na bikin cikar jihar Kaduna shekaru 100 da kafuwa, An Kafa jihar kaduna a shekara ta 1917 zamanin gwamna ‘Lord Lugard’.

Legit.ng ta tattaro cewa, jihar Kaduna dai itace babbar hedkwatar arewacin kasar nan, saboda wannan dalili ya sa hawan ya zama na yankin Arewaci.

Shirye-shirye na hawan daban bikin cikar Kaduna shekaru 100 da kafuwa
Mai martaba sarkin Gombe, (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III

KU KARANTA: Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

A karshen wannan makon ne ake sa ran za a gudanar da tarurruka da bukukuwa iri daban daban don kawo karshen bikin, tare da halartar manyan jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya na jihohin arewacin kasar baki daya da kuma mahayan su cikin kwalliya mai daukar hankalin masu kallo wanda za su gudanar da "Hawan Daba" da nuna sauran al'adun gargajiya da raye-raye irin na kasar Hausa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel