Allahu Akbar: Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa

Allahu Akbar: Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa

Da safiyar yau ne dai muka samu labarin rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya mai suna Alhaji Gidado Idris yana mai shekaru 82 a duniya.

Gwamnan jihar Kaduna ne dai Malam Nasir El-Rufa'I ya fitar da sanarwar a shafin sa na dandalin sadar da zumunta na Facebook inda ya kuma bayyana cewa ya rasu ne a jiya Juma'a.

Allahu Akbar: Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa

Allahu Akbar: Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa

NAIJ.com dai ta samu cewa marigayi Gidado Idris ya riski al'amurra da dama a lokacin rayuwar sa na tarihin Najeriya shekaru da dama da kafuwar ta.

Rahotannin tarihi sun bayyana cewa shine mutumen da ya taimaka wajen gane gawar marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a lokacin da aka kashe shi a yayin juyin mulkin Inyamurai na farko karkashin jagorancin Major Kaduna Nzeogwu a shekarar 1966.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel