Musulmai sun koka da abin da ke faruwa a Makarantun Lauyoyi

Musulmai sun koka da abin da ke faruwa a Makarantun Lauyoyi

- Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya na shan matsin lamba

- Ana dai tursasawa ‘Yan mata cire kallabi da hijabi a Makarantu

- Malaman addini sun fara kira ga Hukuma ta ba kowa ‘yancin su

Labari ya zo mana cewa ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya a halin yanzu kamar yadda wani Malamin addini mai suna Abdullahi Musa Abdul ya bayyana kwanan nan.

Musulmai sun koka da abin da ke faruwa a Makarantun Lauyoyi

Ana addabar matan Lauyoyi su cire kallabi a Najeriya

Arch. Abdullahi Musa yake wani rubutu a shafin sa inda yake nuna yadda ake muzgunawa ‘Yan mata na Musulmai a Makarantun kwarewa a harkar shari’a watau ‘Law School’. Malamin yace ana matsawa mata lamba wajen shigar su.

KU KARANTA: An fara kokarin kawo karshen wahalar man fetur a Najeriya

Ya zama dole mata su cire hijabi yayin da su ka shiga wannan makaranta. Malamin addinin yayi kira da Kungiyoyin addini su jawo hankalin Hukumomin kasar domin a ba mata ‘yancin amfani da kayan da su ka ga dama bisa addinin su.

An yi kira ga Kungiyar Jama’atul Nasril Islam da su yi abin da ya dace domin ganin an kyale mata su yi ibada kamar yadda addinin su ya tanada. Wata Baiwar Allah dai tace ‘ya ‘yan ta na cikin wadanda aka matsawa lamba kwanan nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola
NAIJ.com
Mailfire view pixel