Makamai miliyan 350 marasa rajista ke yawo a Najeriya - UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista ke yawo a Najeriya - UNREC

- Kashi 70 % daga cikin makamai marasa rajista dake yawo a Nahiyan Afrika a hanun yan Najeriya yake inji kungiyar UNREC

- Kungiyar UNREC ta adadin makaman da ke yawo a hanun yan Najeriya abun tsoro ne

- Makamai miliyan 350 mara rajista ke yawo a hanun yan Najeriya

Kungiyar dake kula da zaman lafiya da wanzuwar makamai a nahiyar Afrika karkashin majalisar Dinkin Duniya (UNREC) ta ba da hasake akan yadda makamai mara rajista ke yawu a Najeriya.

Kungiyar (UNREC) ta ce akwai sama da makamai guda miliyan 350 dake yawo a hannun al’ummar Najeriya ba tare da bin ka’aida ba

Makamai miliyan 350 marasa rajista ke yawo a Najeriya - UNREC
Makamai miliyan 350 marasa rajista ke yawo a Najeriya - UNREC

Majalissar dinkun Duniya ta ce, a cikin makamai miliyan 500 da basu da rajista a nahiyan Afrika, kashi 70% na hannun yan Najeriya.

KU KARANTA : An shiga rudani a jihar Ondo yayin da rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji

Hukumar tace wannan al"amari ne mai matukar tayar da hankali.

Darektan UNREC, Mista Anselme Yabouri ya bayyana hakane a lokacin da ya halarci taro akan tsaro a brirnin tarayya Abuja,

Kungiyar UREC tare da hadin gwiwar Kwamitn dake karkashin ofishin shugaban kasa na lura da makamai PRESCOM ta shirya taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel