Mazauna karkara 800 zasu samu kulawar kwararrun likitoci a jihar Kaduna

Mazauna karkara 800 zasu samu kulawar kwararrun likitoci a jihar Kaduna

A yau Laraba 13 ga watan Dasumba, cibiyar kula da lafiyar kunne ta kasa (National Ear Care Centre) ta bayyana cewa, za ta agazawa mazauna karkara 800 a cikin shirin kwanaki uku da zata gudanar a jihar Kaduna.

Shugaba mai rikon kwarya na cibiyar, Dakta Umar Girema, shine ya bayyana hakan da cewa, wannan shirin nasu zai tallafawa al'ummar yankin Birnin Yero dake karkashin karamar hukumar Igabi a jihar.

Girema yake cewa, wannan babbar cibiyar ta lafiya tana da manufar agazawa mutane 800 a yayin aiwatar da shirin ta na kwanaki uku da zata gudanar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufa'i

Yake cewa, za suyi amfani da ranar farko wajen bayar da magunguna, bincikar marasa lafiya tare da tantance wadanda girman cutar su ke bukatar tiyata, sai kuma su aiwatar da aikin na tiyata a ragowar kwanaki biyun karshe.

KARANTA KUMA: Jami'ar Ahmadu Bello ta zamto Zakaran gwajin dafi a Najeriya

Ya ci gaba da cewa, an zabi wannan al'umma ne sakamakon bukatuwa ta yankin su dake neman agajin kulawa da lafiyar su. Ya kara da cewa, an tanadi kwararrun kiwon lafiya guda 30 da zasu aiwatar da wannan shirin wajen tallafawa al'ummar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel